Jiga-jigan jam’iyyar NNPP na daf da shigowa APC—Ganduje

0
37

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace sun kammala shirin karɓar manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP cikin su har da yan majalisun dokokin Najeriya da zasu sauka sheka zuwa APC.

Ganduje, ya kuma bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin wadda ta dauki hanyar mutuwa baki daya.

Ganduje, ya sanar da hakan a ranar Lahadi lokacin daya halarci taron rabon motocin da mataimakan shugaban majalisar dattawa Barau I Jibril, ya gudanar, na motoci 63, da babura 1,137, ga magoya bayan APC a fadin Kano.

Ganduje yace tallafin zai habbaka ayyukan yi ga al’ummar Kano baki daya.

Ganduje ya jinjinawa mambobin jam’iyyar saboda ƙwazon su da biyayya, yana mai nuna tabbacin cewa wasu manyan jiga-jigai, da yan majalisa da sanata daga NNPP za su sauya sheƙa zuwa APC nan ba da jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here