Ya kamata a rika yin gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi ga ma’aurata—NDLEA

0
25

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA tace ya kamata iyayen su rika yiwa yaran su gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi a lokacin da zasu yi aure.

Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana hakan a yau lokacin da yake jawabi a wajen taron gangamin yaki da cin zarafi a tsakanin al’umma da shan miyagun kwayoyi, wanda hukumar wayar da kan yan kasa NOA, ta shirya a jihar Kaduna.

Buba Marwa mai ritaya, yace iyaye sun fi bayar da muhimmanci wajen yin gwajin kwayoyin halitta wato (genotype) dana cuta mai karya garkuwar jiki,  yana mai cewa shima gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi abu ne mai muhimmanci da zai gyara al’umma.

Shugaban hukumar ta NDLEA, yace a wasu guraren ba’a daura aure har sai an gabatar da shaidar lafiyar mace da namiji, sannan yace yin irin haka a fannin miyagun kwayoyi zai rage yawan masu shan kayan maye.

Daily News 24, ta rawaito cewa taron ya samu halartar fitattun mutane da suka hadar da masu rike da mukaman gwamnati dana sarautar gargajiyar, da kuma yan kungiyoyin fararen hula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here