Ƙungiyar dake fafutukar samar da yancin Falasɗinawa ta Hamas ta ce ba za ta ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da Isra’ila ba har sai ta sako fursunonin Flasdinawa sama da 600 kamar yadda aka tsara a yarjejeniya tun da farko.
A ranar asabar data gabata ne Hamas ta miƙa wasu Isra’ilawa 6, don sakin Falasdinawa 600, kamar yadda aka tsara, sai dai kawo yanzu ba’a saki Falasdinawan ba da Isra’ila tayi garkuwa da su.
Firaminista Benjamin Netanyahu, ya ce ba zasu saki Falasdinawan ba har sai Hamas ta saki Isra’ilawa rukuni na gaba.
Ya kuma yi barazanar cewa a kowanne lokaci Isra’ila ka iya cigaba yaƙin da suka kwashe sama da shekara suna yi a Gaza.
A farkon watan Maris yarjejeniyar tsagaita wutar zata ƙare.