Mutane 4 sun kone ƙurmus a hatsarin mota a Jigawa

0
34

Wani hatsarin mota daya faru a karamar hukumar Gwaram yayi sanadiyyar mutuwar mutane 4 da jikkata wasu 10, lokacin da motar da suke ciki kirar Hummer, ta kama da wuta.A jiya Asabar da misalin karfe 4 na yamma lamarin ya faru a kusa da makarantar sakandiren yan mata ta haɗaka dake Gwaram.

Wata sanarwa da kakakin ‘yansanda na jihar SP Lawan Adam ya fitar a yau Lahadi ta bayyana cewa motar ta tashi daga ƙaramar hukumar Zaki ta jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke ƙaramar hukumar Gwaram.

Sanarwar ta ce, motar tana ɗauke da fasinjoji 44, manya 25 da yara 19.

Kakakin ‘yansandan ya ce, wutar ta kama sakamakon katifa da aka ɗaure a bayan motar da ke kusa da salansa.

Sanarwar ta ƙara da cewa mutum goma da suka ji rauni an kai su asibitin Gwaram yayin da sauran aka yi nasarar tserar da su daga motar ba tare da wani rauni ba.

Waɗanda suka rasun kamar yadda sanarwar ‘yansandan ta nuna su ne Zuwairah Hassan, mai shekara 40 da Fatima Hassan, mai shekara 5 da Iyatale Hassan mai shekara 3 da Halima Muhammad mai shekara 10, dukkanninsu daga ƙauyen Saldiga da ke yankin ƙaramar hukumar Zaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here