Cikakken jawabi akan hudubar Sheikh Bin Usman ta yau Juma’a

0
84

Sheikh Muhammad Bin Usman, ya jagoranci gabatar da Sallar Juma’a a Masallacin Sahaba dake unguwar Kundila.

Hakan ya biyo bayan yadda majalisar malaman Kano karkashin jagorancin Malam Ibrahim Khalil, ta samar da sasanci tsakanin Sheikh Muhammad Bin Usman, da hukumar Masallacin jami’ur Rahman, bayan da aka samu rikici tsakanin Bin Usman da hukumar gudanarwar Masallacin.

A yayin hudubar ta yau, Malamin ya fara da yin jan hankalin akan yadda za’a yi tashin alkiyama musamman yadda kasa zata bayyana abubuwan da dan adam ya gabatar a rayuwar duniya.

Bayan haka, Sheikh Bin Usman, yaja hankalin al’umma dasu kiyaye aikata laifukan da Ubangiji zai yi fushi dasu.

Bugu da kari, Sheikh Muhammad Bin Usman, ya roki al’ummar Musulmai yan kasuwa dasu saukakawa juna lokacin da azumin watan Ramadan ke gabatowa, yana mai cewa Allah yana jin Ƙan wanda yaji kan bayin sa.

Haka zalika ya nemi a yi kokarin dagewa da ibada a watan Ramadan.

Cikin hudubar ya kuma yabawa majalisar malaman Kano karkashin jagorancin Malam Ibrahim Khalil, bisa yadda ta samar da sulhun rikicin daya taso tsakanin sa da hukumar gudanarwar Masallacin jami’ur Rahman, wanda har sai da aka kai ga dakatar da limancin Bin Usman a Sabon Masallacin jami’ur Rahman.

Malamin yace bai amince a zagi duk wanda yaci mutuncin sa ba, saboda akwai ranar da Allah zai yiwa kowa hisabi.

Daga karshe Sheikh Muhammad Bin Usman, ya mika godiyar sa ga kwamitin Masallacin Sahaba, da yan agaji har ma da daukacin al’umma bisa kokarin da suke yi a Masallacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here