Kisan dalibai 5 ya janyo rufe jami’ar tarayya dake Lokoja

0
14

Hukumar gudanarwar jami’ar tarayya ta Lokoja dake jihar Kogi, ta dauki matakin rufe jami’ar har sai baba ta gani biyo bayan kisan daliban makarantar 5, sakamakon wani hadarin motar Tirela daya rutsa dasu a ranar litinin 17 ga Fabrairu.

Lamarin ya faru a yankin Felele dake birnin jihar Kogi.

:::Dan majalisar NNPP ya koma jam’iyyar APC

Matakin ya biyo bayan zanga-zangar da dalibai suka yi a ranar Laraba, inda suka rufe kofar shiga jami’ar domin bayyana bacin ransu akan hatsarin.

Magatakardar jami’ar Rebecca Okojie, ce ta sanar da rufe jami’ar cikin sanarwar data fitar inda tace hakan ya zama wajibi don hana zanga-zangar zama wani babban rikici.

Sanarwar tace duk da gwamnati ta shiga lamarin hakan bai sanya daliban kwantar da hankalin su ba, wanda tuni aka bawa kowanne dalibi umarnin fita daga mazaunin sa daga karfe 12, na rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here