Masu gidajen Burodi a jihar Kano sunce ba zasu rage farashi ba, duk da cewa farashin fulawa ya sauka a kasuwa.
Kungiyar masu gidajen Burodin, tace har yanzu ana fuskantar tsadar man girki, Sukari, da makamashi, wanda sune ginshikin samar da Burodi.
Sai dai kungiyar tace zata kara girman Burodin tare da cigaba da siyarwa akan farashin sa na yanzu.
Bayanin hakan yazo cikin wata sanarwar bayan taron da hukumar karbar koke-koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta fitar bayan ganawa da Kungiyar masu gidajen Burodin akan dalilin da yasa har yanzu basu rage farashin kayan su ba, bayan cewa an samu raguwar farashin fulawa sosai.