Iran ta yanke hukuncin kisa akan daruruwan mutane

0
85

Gwamnatin Iran, ta zartar da hukuncin kisa akan mutane 975, a shekarar 2024.

Mafi yawancin wadanda aka yankewa hukuncin an same su da laifin safarar miyagun kwayoyi, sai kuma wadanda aka kashe bisa samun su da laifin kisan kai.

Masu rajin kare hakkin bil adama, ne suka sanar da hakan a yau Alhamis, tare da cewa hakan babban abin damuwa ne a rika yanke hukuncin kisa ga mutanen da suka aikata wasu laifuka.An samu karin kaso 17 cikin dari na adadin kisan da mahukuntan kasar keyi in aka kwatanta da shekarar 2023, inda aka zartar da hukuncin kisa ga mutane 834.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Oslo, wadda take karkashin mutanen kasar Faransa ta kalubalanci gwamnatin Iran, dangane da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here