Attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote, ya zama mutum na 86, cikin jerin mutanen da suka fi kowa kudi a duniya.
Kafin yanzu Dangote yana kan mataki na 144.
:::An dakatar da Bellingham daga buga wasannin gasar Laliga
Mujallar Forbes, tace a yanzu haka Attajirin na Afrika, yana da dukiyar da darajar ta takai Dala biliyan 23.9.
A ranar litinin data gabata ne mujallar ta zanta dashi inda yace ya fuskanci kalubale mai yawa a yayin da yake kokarin gina matatar man fetur a Najeriya.
A cikin bayanan sa Dangote, yace bai taba fuskantar hatsari da kasada ba, irin wanda ya fuskanta wajen gina matatar, yana mai cewa da matatar bata kai ga nasarar fara yin aiki ba zai iya rasa rayuwar sa baki daya.
Attajirin ya kashe kudin da yakai Dala biliyan 23, wajen gina matatar.