Gwamnatin Najeriya ta rike albashin ma’aikatan ofisoshin jakadancin ta

0
42
Tinubu
Tinubu

Ma’aikata 450 dake aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen ketare sun shafe watanni 6 ba tare an biya su albashi ba.

Jaridar punch, tace wannan abu yasa ma’aikatan sun kasa biyan kudin hayar gidajen su da Kudin makarantun yara da sauran bukatun rayuwar yau da kullum.

:::Majalisar Malaman Kano ta yanke hukunci akan Masallacin Sahaba

Mutanen da abin ya shafa suna yin aiki a ofisoshin jakadancin Najeriaya a kasashen ketare guda 109.

Mai rikon mukamin jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar harkokin waje ta kasa Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar da rashin biyan albashin inda yace suna sane da hakan kuma ana yin aiki domin magance matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here