Jamhuriyar Nijar ta hana ‘yan Najeriya masu yin amfani da Fasfo din tafiye-tafiye na Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS shiga cikin cikin kasar.
Hakan ya biyo bayan yadda kasar ta fara aiwatar da sabbin takkukuman tafiye-tafiye ga yan Najeriya masu amfani da Fasfo din kungiyar ECOWAS.
Jamhuriyar Nijar ta dauki hukuncin ne bayan da ta fice daga ECOWAS, tare da kasashen Mali, da Burkina Faso.
Duk da cewa Nijar bata rufe iyakokin ta da Najeriya ba, amma ta dauki tsauraran matakai musamman a iyakokin Illela da Konni.
Matafiya daga kasashen biyu musamman yan kasuwa sun fara shiga damuwa akan wannan matsala ta diflomasiyya dake tsakanin Najeriya da Nijar.