Hauhawar farashin kayyakin masarufi ta sauka zuwa kaso 24.48

0
80

Kamar yadda NBS tace an samu saukin rayuwar ne a watan Junairu na shekarar 2025.

Hukumar Ƙididdiga ta kasa (NBS) ce ta sanar da hakan a yau Talata, kamar yadda shugaban ta Adeyemi Adeniran, ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labarai, inda yace saukin ya samu biyo bayan sake bibiyar yanayin hauhawar farashin kayyakin masarufi na kasa don daidaita shi da tsarin sauran kasashen duniya.

A kwanakin baya sai da yanayin hauhawar farashin kayyakin masarufi na Najeriya yakai kaso 34.80, cikin dari.

Tuni dai aka bayar da rahoton saukar farashin kayayyakin masarufi musamman abinci, a wasu kasuwannin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here