Alhaji Aliko Dangote, yace gina matatar man fetur da yayi shine babban hatsarin daya taɓa fuskanta a rayuwar sa.
Dangote, yace da matatar bata fara aiki zai iya mutuwa.
Attajirin ya kashe kudin da yakai Dala biliyan 23, wajen gina matatar.
Ya sanar da hakan a jiya litinin lokacin da yake zantawa da mujallar Forbes, sannan yace ya fuskanci kalubale iri iri a kokarin samar da matatar.