Kotu ta hana gwamnatin tarayya rike kudin kananun hukumomin Kano

0
111
Kano

Babbar kotun jihar Kano, ta hana gwamnatin tarayya yin katsalandan akan kudaden kananun hukumomin jihar 44.

Mai shari’a Musa Ibrahim Karaye, ne ya yanke hukuncin hana gwamnatin tarayyar rike kason kananun hukumomin yayin zaman kotun na yau litinin.

:::Malaman addini na neman kwace siyasa daga hannun yan siyasa—Sule Lamido

Mambobin jam’iyyar APC, reshen Kano, ne suka shigar da kara tun da farko suna neman a hana kananun hukumomin kason su na tarayya bisa hujjar cewa an gudanar da abubuwan da suka ci karo da ka’ida a lokacin gudanar da zabukan kananun hukumomin jihar a watan Oktoban 2025.

Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas da Aminu Aliyu Tiga, ne suka shigar da karar.

Sannan a zaman kotun ta sahalewa daukacin kananun hukumomin damar yin amfani da kudaden su ba tare da wani shinge ba.

Lauyan dake kare kananun hukumomin Bashir Wuzirchi, ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga jihar Kano.

Sai dai kakakin APC na Kano Ahmad Aruwa, yace zasu daukaka kara saboda basu amince da hukuncin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here