Gwmanan jihar Kaduna Uba Sani, yace jam’iyyar APC tana samun farin jini a Najeriya sakamakon cewa tana gudanar da mulkin adalci ga yan kasa, tun daga jihohi zuwa tarayya.
A jiya Asabar ne gwamnan ya bayyana haka lokacin da yake karÉ“ar wasu manyan yan siyasa 50, da suka canja sheka daga wasu jam’iyyun zuwa APC a Kaduna.
Uba Sani, ya bayyanawa wadanda suka canja shekar cewa za’a yi tafiyar siyasa dasu kamar kowanne dan APC, babu banbanci.
Daga cikin wadanda su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yero, Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi, dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata da kuma Alhaji Sani Sha’aban.
Sauran sun hada da Sanata Danjuma Laah, da Abubakar Mustapha, tsohon sakataren jam’iyyar PDP na kasa da Ambasada Sule Buba, tsohon wakilin Najeriya a Koriya ta Kudu.
An karbi mutanen a dandalin Murtala Square, a ranar asabar..