Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, murnar cika shekaru 65 da haihuwa.
A sakon taya murnar cika shekaru 65, Tinubu ya mika jinjinar sa ga El-Rufai kan bada gudunmawar cigaban dimokuraÉ—iyya a Najeriya.
Yace El-Rufa’i malami ne kuma dan siyasa mai hazaka.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, Tinubu ya yaba da rawar da El-Rufai ya taka a matsayin wanda ya bada gudunmawa wajen kafa jam’iyyar APC da kuma gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zabuka uku a jere.
Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yau Lahadi.
Sanarwar tace shugaban kasa ya yaba da rawar da Malam El-Rufai ya taka a fafutukar da aka yi kafin kafa jam’iyyar APC da kuma gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a 2015, 2019, da 2023.