NNPCL ya musanta siyar da fetur mara inganci

0
80

Kamfanin mai na kasa NNPCL ya musanta iƙirarin da wani mutum ya yi na cewa fetur din da kamfanin ke siyarwa bai kai na matatar Dangote auki ba, saboda yana saurin karewa a lokacin amfani dashi.

Cikin wani faifan bidiyo da yayi yawo a shafukan sada zumunta an ga wani mutum da ya ce ya sayi man fetur daga kamfanin NNPCL a kan farashin naira 945, sannan ya sayi wani man a wani gidan mai da ke siyar da man Dangote, a kan naira 925.

A cikin bidiyon mutumin ya yi iƙirarin cewa man Dangote ya zarta na kamfanin NNPCL daɗewa ana amfani da shi, sannan yace ya gwada mayukan biyu a injuna biyu, daga ƙarshe na NNPCL ya riga na Dangote ƙarewa da minituna fiye da 10.

Amman NNPCL ya ce gwajin da mutumin ya yi bai yi shi da ƙwarewa ba, sannan babu wata hujja a cikinsa.

Sanarwar da NNPCL ya fitar tace mafi yawan man da wannan gidan mai na NNPCL da mutumin ya yi iƙirarin sayo man daga kamfanin Dangote yake kawo mai

NNPCL, yace ba zai amince da irin wannan kazafi ba, Kuma zai rika daukar mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here