Rikici tsakanin mayakan Boko Haram da mayakan ISAWAP yayi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda masu yawa a yankin Malam Fatori.
Wata Majiya ta tabbatar da cewa rikicin ya faru a ranar alhamis tsakanin yan Boko Haram masu biyayya ga Bakoura, da kuma yan ISAWAP, wanda mayakan da yawa suka rasa rayukan su.
Mai sharhi da bayar da bayanai a kan ayyukan tsaron yankin tafkin Chadi Zagazola Makama, yace an yi rikicin a gabashin Malam Fatori dake jihar Borno kusa da iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar, zuwa gabashin Boso.
Majiyar tace fadan ya sanya gomman yan ta’adda mutuwa sannan wasu da dama sun samu munanan rauni.
Rikicin ya samo asali daga batun wanda yake da iko da yankin da fadan ya kaure, kuma wannan abu ya sanya an gano maboyar yan ta’addan da samun bayanai akan su.