An gudanar da Sallar Juma’a karkashin kulawar jami’an tsaro a Masallacin juma’a na Sahaba

0
101

An zube jami’an tsaro masu yawa a hanyar shiga Masallacin juma’a na Sahaba dake unguwar Kundila.

Hakan baya rasa nasaba da rikicin limancin Masallacin tsakanin Sheikh Muhammad Bin Usman, da hukumar gudanarwar Masallacin data dakatar dashi daga limancin.

Idan za’a iya tunawa a ranar larabar data gabata ne aka samu fitar wata sanarwa mai nuni da cewa Sheikh Muhammad Bin Usman, ne zai jagoranci Sallar juma’a a yau 14 ga watan Fabrairu. Amman an iske jami’an tsaro, tare da bayyana Sheikh Sayyid Ibrahim Inuwa, a matsayin wanda ya jagoranci Sallar.Da farko Sheikh Muhammad Bin Usman, sanar da cewa shi zai jagoranci sallar Juma’a a masallacin bayan dawowa daga tafiyar da ya yi zuwa Æ™asar waje. 

Mun tuntubi shugaban sashin kafafen sada zumunta na Masallacin Sahaba dake unguwar Kundila, bangaren Sheikh Muhammad Bin Usman, Shamsuddeen Sulaiman Usman, don jin abinda ya hana Bin Usman, gabatar da Sallar a yau, sai dai bamu samu damar zantawa dashi ba, saboda bamu same shi a kiran wayar da muka yi masa ba.

Ko a lokacin da aka dakatar da Sheikh Muhammad Bin Usman, Shamsuddeen Sulaiman Usman, yace basu amince da dakatarwar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here