Fursunoni sun lashe gasar Musabaƙar Al-Qur’ani a jihar Kano

0
75

Mutane uku daga cikin fursunonin dake daure a jihar Kano sun samu nasarar lashe gasar Musabakar Al-Qur’anin da aka shirya musu.

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta  ƙasa reshen jahar Kano ce ta shirya gasar a wani yunkurin samar da ilimi ga daurarrun.

Mai magana da yawun hukumar gidajen yari ta Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce an shirya musabakar ce domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari.

Ya bayyana cewa fursunan da ya lashe gasar ana tsare dashi ne a gidan gyaran hali na Kumawa, inda ya samu kyautar Naira dubu dari.

Na biyu kuma a Gidan Yarin Goron Dutse ya samu kyautar Naira dubu 50.

Mutum uku yana tsare ne a Gidan Yarin da ke Janguza ya samu kyautar Naira dubu ashirirn.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Kungiyar Alarammomi, Gwani Shuaibu Shehu, ya yaba wa shugaban hukumar Gidajen Yari na Jihar Kano wajen shirya musabakar.

A nasa jawabin, shugaban hukumar hukumar gidajen gyaran hali na Kano, Ado Inuwa, ya bayyana godiyarsa ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bisa halartar gasar musabakar da yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here