Hukumar NCDC mai dakile yaduwar cutuka ta kasa, ta sanar da cewa cutar zazzabin Lassa ta kashe mutane 70, a kasar nan cikin watannin farko na wannan shekara.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce mutum 1,552 ne ake zaton sun kamu da cutar, yayin da aka tabbatar da cewa mutane 358 sun kamu.
An fi samun cutur a jihohi 10, cikin kananun hukumomi 58.
Jihohin da aka fi samun asarar rayuka sakamakon cutar sun haÉ—a da Taraba inda mutum 18 suka mutu, sai Ondo mai 17 da Edo mai 11 sai Bauchi da Ebonyi masu 6 kowanne da Gombe mai 5, sai Kogi mai 4 da kuma jihohin Nasarawa da Plateau masu uku jimilla.
Rahoton na NCDC ya kuma nuna cewa jihohin Ondo da Edo da Bauchi ne ke da kashi 75 cikin 100 na waÉ—anda aka tabbatar suna É—auke da cutar.
ZazzaÉ“in Lassa dai cuta ce da ake kamuwa da ita daga mu’amala da wasu dabobbi dangin É“eraye, ko cin abincin da suka taÉ“a.