Najeriya na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake mulki – Obasanjo

0
101

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da mulki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito tsohon shugaban na wannan maganar a wurin taron bikin cikar makarantar Kings college ta Legas – daya daga cikin tsoffin makarantu a kasar – shekara 113 da kafuwa.

Mista Obasanjo wanda shi ne ya jagoranci taron ya ce ”Kishin kasa shi ne tubalin jagorancin al’umma, sannan kuma raunin jagoranci shi ke haifar da rashin adalci..”

Ya kara da cewa ”Ba za mu yadda da kanmu ba, bayan mun rasa kwarin gwiwwa, domin kuwa a duk inda aka rasa kwarin gwiwwa to lallai an rasa hadin kai”.

”Idan ba mu da kyakkyawar manufa, to mene ne makomar matasanmu? Wane hobbasa za su iya yi? Dole da farko mu sanya kishin kasa a ranmu, sannan ko ma mene ne ya biyo baya” in ji Obasanjo.