Hatsarin Tirela ya kashe mutane 16 a Kano

0
134

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC, tace mutane 16 ne suka rasu sakamakon kifewar wata Tirela a cikin gadar karkashin ƙasa ta Muhammadu Buhari, dake unguwar Hotoro a birnin Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar reshen  jihar Kano, Abdullahi Labaran, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar, inda ya ce hatsarin ya afku a daren ranar Alhamis a kan babbar gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro.

Abdullahi Labaran ya ce lamarin ya faru sakamakon gudu da direban motar ke yi, lamarin da ya sa ta ƙwace masa.

Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 71 da motar ke ɗauke da su yayin da mutum 52 suka samu raunuka, mutum 16 kuma suka mutu.

Yace an kai waɗanda suka jikkata asibitin Murtala domin ba su kulawar da ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here