Shugaban Kasa Tinubu ya sauka a Habasha

0
65

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya sauka a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, don halartar taron kungiyar hadin kan Afrika AU karo na 38.

A ranar  14 zuwa 18 ga watan Fabrairu aka shirya gudanar da taron wanda zai samu halartar shugabannin kasashen Afrika, don tattaunawa akan abubuwan kasashen su ke bukata.

Mai taimakawa shugaban a fannin yada labarai Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar a safiyar yau juma’a.

Mataimakin shugaban tsare tsare na fadar shugaban kasar Habasha Eshetu Legesse, ne ya tarbi Tinubu, tare ministan harkokin waje na Najeriya Yusuf Tuggar, sai kuma mai kula da ofishin jakadancin Najeriya a Ethiopia Nasir Aminu.

Tinubu, ya zarce Ethiopia ne daga ziyarar da ya kai kasar Faransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here