Gwamnan jihar Kano ya bayyana jimamin sa akan rasuwar Dan Zago

0
36

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jimamin sa akan rasuwar Alhaji Ahmadu Haruna Dan Zago, shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano daya rasu a yau Alhamis.

Daraktan yada labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar.

:::Kundin adana tarihi na Guinness ya tabbatar da bajintar Hilda Baci

Dan Zago, ya rasu yana da shekaru 74, a duniya, sannan ya bar Mata 4 da yaya 37 maza da mata, da kuma tarin jikoki.

Sanarwar ta kara da cewa Marigayin ya bar duniya da sanyin safiyar yau Alhamis bayan yayi fama da jinya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Wata majiya daga iyalan Dan zago, tace za’a yi masa jana’iza a fadar mai martaba sarkin Kano da misalin karfe 1:00, na rana.

Sanarwar gwamnatin tace gwamna Abba, ya bayyana matukar bakin cikin sa lokacin daya samu labarin rasuwa yana mai cewa Dan zago, ya bayar da lokacin sa wajen samar da cigaban jihar Kano a shekaru 50, da suka gabata.

Marigayi Alhaji Ahmadu Haruna Dan zago, fitaccen dan siyasa ne, kuma dan kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here