Kundin adana bajinta na Guinness ya karrama dan Najeriaya akan daukar hoto

0
118

Dan Najeriya mai suna Sa’idu Abdulrahman, dan asalin jihar Yobe, ya lashe kambun nuna bajinta daga kundin Guinness World Record, mai bibiya da kuma adana abubuwan bajintar da mutane ke aiwatarwa a fadin duniya.

:::Dattawan arewa sun sake neman Tinubu ya janye kudurin dokar haraji

Sa’idu, ya samu damar lashe kambun bayan ya nuna bajintar daukar kananun hotuna 897, a cikin mintuna 60 kacal.

An gabatar da karramawar ta hannun wakilan Guinness World Record, a gidan gwamnatin jihar Yobe, a ranar laraba inda aka bayyana kambun ga gwamna Mai Mala Buni.

Mai Mala, yace wannan abu da dan jihar tasa yayi abin a yaba ne kuma zai kara zaburar da sauran matasa wajen yin abubuwan da za’a yi alfahari dasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here