Kudirin dokar haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar Wakilai

0
60

Kudirin dokar haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi akan sa da yan majalisar suka yi yayin zaman ta na yau laraba.

Farfesa Julius Ihonvbere, ne ya zama shugaban muhawarar da aka tafka kan kudirin, yana mai cewa dokar zata inganta harkokin harajin Najeriya.

Tun da farko majalisar ta haɗe duka ƙudurorin harajin huɗu da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike mata a shekarar da ta gabata zuwa ƙuduri guda kafin fara muhawara a kansa.

:::Babban turken wutar lantarkin Najeriya ya durkushe

Farfesa Julius Ihonvbere, shine shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan, ya kuma bayyana godiyar sa ga kungiyar gwamnonin kasa bisa amincewar da tayi wa kudirin, bayan yi masa gyaran fuska wajen cire wasu abubuwan da basu aminta dasu a cikin kudirin dokar.

Mafi yawa daga cikin al’ummar arewa na kalubalantar kudirin dokar harajin bisa tsoron da suka bayyana na zargin tauye hakkin yankin da suka ce ana shirin yi a karkashin kudirin dokar.

Idan za’a iya tunawa shugaban kasa Tinubu, ya sha alwashin tabbatar da kudirin duk da cewa yana shan suka musamman daga masana tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here