Majalisar dattawa tayi barazanar kin amincewa da kasafin yan sanda na shekarar 2025

0
38

Majalisar dattawa tayi barazanar kin amincewa kasafin kudin rundunar yan sandan kasa na shekarar 2025 saboda ɓatan bindugu 178,459, a hannun jami’an yan sanda.

Rundunar yan sandan tace yan fashi da yan ta’adda ne suka kwace bindugun a hannun jami’an ta.

:::Gwamnatin Neja zata karya farashin Abinci saboda Azumin Ramadana

Mataimakin shugaban kwamitin asusun gwamnati a majalisar dattawa Peter Nwaebonyi, ne ya bayyana hakan, bayan samun rahoton ɓatan kananun bindugu 3,907, daga hannun yan sandan.

Ya sanar da hakan ne a yau laraba lokacin da ake zantawa dashi a talbijin ta Channels, sannan yace dole ne a binciko inda aka kai bindugun in har rundunar yan sandan tana son majalisa ta sahale kasafin kudin ta.

Babban Sufeton yan sandan kasa Egbetokun, ne ya sanar da majalisar cewa an rasa makaman sakamakon ayyukan yan fashi da kuma yan ta’addan dake kaiwa yan sanda hari.

Idan za’a iya tunawa dai a shekarar 2019, ne mai binciken kudi na gwamnatin tarayya, ya sanar da cewa an sace bindugun rundunar yan sandan Najeriya da yawan su yakai 178,459, kuma har yanzu ba’a san inda suka shiga ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here