Daya daga cikin mambobin majalisar wakilai na jam’iyyar PDP, Salisu Garba Koko, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.
Garba Koko, shine ke wakiltar mazabun Besse/Maiyama Yema, dake jihar Kebbi.
:::Wadanda suka sace daraktan mulki na APC a matakin kasa sun nemi Naira miliyan 350
Kakakin majalisar Tajuddeen Abbas, ne ya bayyana ficewar Koko, cikin wata wasikar daya karanto yayin zaman majalisar na yau laraba.
Dan majalisar yace rikicin cikin gidan daya mamaye PDP, kuma aka gaza magancewa tsawon lokaci shine dalilin sa na sauya shekar.
Amman shugaban marasa rinjaye na majalisar Kingsley Chinda, yace babu wani rikicin da ya yiwa PDP katutu.