Gwamnatin Jigawa zata dauki jami’an tsaro 9,970

0
75

Gwamnatin Jigawa ta amince da shirin daukar mutane 9,970, aiki don bayar da tsaro ga al’umma da sauran gine-ginen gwamnati a fadin jihar.

:::Najeriya ce kasa ta 140 a jerin kasashe masu aikata cin hanci da rashawa a duniya

Kwamishinan yada labarai, wasanni, matasa da al’adu Sagir Ahmad, ne ya sanar da hakan a yau Talata, yana mai cewa an amince da bukatar daukar ma’aikatan ne a yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar daya gabata.

Yace kwamitin samar da tsaro a makarantu, asibitoci, da kotuna ne ya bayar da shawarar daukar jami’an tsaron.

Yayin zaman majalisar an amince cewa hakan zai tabbatar da inganta tsaro a makarantun Firamare da Sakandire, da manyan kotunan Jigawa, da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko, sai kuma manyan asibitocin jihar.

Sanarwar da kwamishinan ya fitar tace wannan yunkuri zai samar da ayyukan yi da kuma dakile bata gari masu sha’awar samarwa al’umma rashin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here