Kungiyar dake bin diddigin aiwatar da harkokin kudi a bayyane ta duniya (Transparency International) tace Najeriya ce ta samu gurbi na 140, a jerin kasashen da ake aikata cin hanci da rashawa a fadin duniya a shekarar 2024.
:::Abin kunya ne ace Najeriya ba zata iya ciyar da al’ummar ta abinci ba—Gwamnan Bauchi
Kungiyar ta sanar da hakan cikin wani rahoton data fitar a yau Talata, inda tace kasar Denmark, ce tafi fuskantar ayyukan cin hanci da rashawa a 2024.
Rahoton yayi amfani da nazari akan yan kasuwa da masana, da kuma yin duba akan ingancin zabukan kasashe sai kuma yin duba akan yanayin tafiyar da hukumomin gwamnati na kasashe 180, wajen bayyana rahoton nata.
Kungiyar tace Najeriya, Mexico, Madagascar, Uganda, Iraqi da Kamaru sun samu maki 26, cikin 100, a ma’aunin da tayi amfani dashi wajen bayyana sakamakon binciken ta.
Sai dai kuma an sanar da kasashen Somaliya, Venezuela, da Sudan ta Kudu, a matsayin inda aka fi tafka cin hanci da rashawa a shekarar data gabata.