Dan majalisa mai wakiltar mazabun Jaba da Zangon Kataf, Amos Gwamna Magaji, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC.
Dan majalisar wanda shine shugaban kwamitin kula da harkokin lafiya na majalisar wakilai ya sanar da cewa ficewar tasa ta samo nasaba akan yadda rikicin cikin gida ya dabaibaye PDP, har aka kasa warwarewa tsawon lokaci, tun daga karamar hukuma har zuwa matakin shugabancin jam’iyyar a matakin kasa.
:::Gwamnatin tarayya ta ninka kudin rijistar kafa jami’o’i masu zaman kansu da kaso 400 cikin dari
Amos, yace yana da tabbacin bayar da gudunmawar sa wajen inganta harkokin siyasar APC a mazabun da yake wakilta.
Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar Kingsley Chinda, ya kalubalanci sauyin shekar da Amos, yayi inda ya nemi kakakin majalisar wakilai ya ayyana kujerar dan majalisar a matsayin wadda aka kwace daga hannun sa don zabar sabon dan majalisar da zai wakilci Jaba da Zangon Kataf.
Kingsley Chinda, yace Amos Gwamna bai bi ka’ida ba wajen sauya shekar tasa.