Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, yace abin kaico ne ace Najeriya tana shan wahala wajen ciyar da al’ummar ta abinci, duk da cewa kasar tana da albarkatun noma da bai kamata ace tana fama da karancin abinci ba.
Daily News 24, ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Portugal a Najeriya Paulo Martins, a fadar gwamnatin jihar, inda yace wannan abu na karancin abinci a Nigeriya abin kunya ne saboda an gaza samun isasshen abinci ga al’ummar kasar su kusan miliyan 250.
:::Shugaban kasar Amurka na neman lalata yarjejeniyar tsagaita wutar yakin Isra’ila da Hamas
Bala Muhammad, yace mayar da hankali a fannin amfani da dabarun noma na zamani da zuba jari a fannin aikin gona zai taimaka wajen magance matsalar rashin abincin da ake cigaba da fuskanta.
Ya kuma bayyanawa jakadan na kasar Portugal, cewa Bauchi tana da isashshen filin noman da yan Portugal, zasu iya zuba hannun jarin su a fannin aikin gona ba tare da fuskantar wani kalubale ba, daya danganci cin hanci, ko haraji mai yawa.
A nasa jawabin Paulo Martins, yace ya ziyarci jihar ce bayan tattaunawa da wakilan Bauchi, a majalisar dokokin kasa inda suka bayyana masa cewa akwai abubuwan alkairin da jihar zata samar in tayi hadin gwuiwa da Portugal.