NDLEA ta kama Maza da Mata su 80 masu shan kayan maye a bikin Birthday a jihar Kano

0
71

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, taja hankalin iyaye su kula da tarbiyyar yayan su sosai, akan cewa sun kama wasu yan Mata 30 da Maza 50, masu shan kayan maye da sunan murnar Birthday.

Daily News 24, ta rawaito cewa Kakakin hukumar Sadik Muhammad Maigatari, ne ya sanar da hakan bayan bayyana bidiyon matasan a shafin sa na Facebook, a safiyar yau Talata.

Yace sun samu nasarar kama matasan tun a watan daya gabata, bayan samun su da laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi a wani wajen bikin zagayowar ranar haihuwa.

Sakamakon haka NDLEA, ta nemi iyayen matasa Maza da Mata su saka ido a yanayin ma’amalar yayan su don kaucewa fadawa mummunan halin shaye-shaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here