Babbar kotun tarayya dake Abuja ta sanar da jingine sauraron shari’ar da take yiwa jagoran kungiyar IPOB masu rajin kafa kasar Biapra Nnamdi Kanu.
Mai shari’a Binta Nyako, ce ta bayyana daukar matakin dakatar da shari’ar bayan gabatar mata da Kanu, a yau Litinin.
Jingine sauraron shari’ar yazo bayan da Kanu, ya kafe akan cewa mai shari’a Binta Nyako, ba zata cigaba da yi masa shari’a ba tunda a baya ta bayyana janye hannu ta daga sauraron shari’ar.
Gwamnatin tarayya dai ita ta shigar da karar Nnamdi Kanu, bisa zargin sa da laifin cin amanar kasa.