Saudiyya ta dakatar da bayar da Visa ta kasuwanci ga yan Nigeria

0
116

Gwamnatin kasar Saudiyya ta jingine bayar da shaidar shiga cikin kasar ta yin kasuwanci ga wasu kasashen duniya 14, cikin su har da Nigeria.

An dakatar da bayar da bizar ce don samun damar dakile al’adar wasu mutane masu shiga kasar da shaidar yin kasuwanci amma daga bisani su zauna har sai sun gudanar da aikin Hajji.

Gwamnatin Saudiyya tace hakan yana haifar da cunkoson mutane a yayin gudanar da aikin hajji a kowacce shekara, saboda ana gaza samun cikakken bayani akan adadin masu yin aikin Hajjin.

Tuni kasar ta fara aiwatar da wannan doka a watan Fabrairu da muke ciki akan Ƙasashen Nigeria, Algeria, Bangladesh, Ethiopia, India, Indonesia, Iraq, Jordan, Morocco, Pakistan, Yemen, Tunisia, da kuma kasar Sudan.

Ko a shekarar data gabata sai da Saudiyya tace zata kama mutanen wadannan kasashe 14, in suka yi aikin hajji ba tare da yin rijista ba.

A cewar kamfanin tafiye-tafiye na TravelBiz, Saudi Arabia zata riƙa baiwa al’ummomin ƙasashen 14 ne bizar kwanaki 30 kuma idan ta ƙare babu zaɓin tsawaitawa face ficewa daga ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here