Gwamnan Zamfara ya janye kalaman sa akan kin jinin sulhu da yan bindiga 

0
41

Gwamnan jihar Zamfara Dr. Dauda Lawan Dare, yace zai yi sulhu da yan bindiga.

Gwamnan yace zai yi sulhun dasu ne kawai idan sun ajiye makaman su tare da mika wuya.

Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kafar BBC.

A baya dai gwamnan ya sha nanata cewa gwamnatin sa ba zata taba yin sulhu da yan ta’adda masu kashe al’ummar jihar ba, bisa hujjar cewa sun cutar da al’umma da yawa kuma a lokacin sulhu azo a basu kudi.

Dauda yace akwai wadanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai an duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, da dangin su bawai kullum a riƙa fitfita ƴan bindiga ba.

Gwamna Dauda ya bayyana cewa suna samun nasara a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga, inda yace an kashe ƴan ta’adda fiye da 50 a ranar Juma’a a garin Tingar Fulani, wajen Zurmi da Shinkafi.

Amman a yanzu yace sulhun abu ne mai kyau inde an yi shi ta hanyar data dace.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewa masu fama da ayyukan yan ta’adda masu yin garkuwa da mutane da satar dabbobi, har ma da kisan al’umma babu wani dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here