Ma’aikatan manyan makarantu zasu shiga yajin aikin a jihar Nasarawa 

0
53

Daukacin ma’aikata masu koyarwa da marasa koyarwa na makarantun gaba da sakandire a jihar Nasarawa zasu shiga yajin aiki saboda kin fara biyan su tsarin mafi karancin albashi na naira 30,000.

Kungiyar gamayyar ma’aikatan (JUNSTI) tana kuma neman gwamnatin jihar ta amince da sabon tsarin mafi karancin albashi na naira dubu 70 wanda gwamnatin tarayya da wasu jihohin suka fara aiwatarwa.

Manyan makarantun da yajin aikin zai shafa sun hadar da kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha dake Lafia, sai kwalejin Noma da kimiyya da fasaha ta  Lafia, da Kuma kwalejin ilimi dake Akwanga.

Shugaban kungiyar ma’aikatan Samson Kale-Gbande, da sakataren sa Paul Olota, ne suka sanar da hakan cikin wata sanarwa, da suka ce gwamnatin jihar bata yi musu karin albashi ba ko kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here