Gwamnatin Kebbi Zata Sake Aurar da Maza da Mata 600

0
63

Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu,  ya sanar da ware naira million 54 a matsayin sadakin ma’auratan mata 300, maza 300 da za’a aurar daga daukacin kananun hukumomin jihar kebbi.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan jihar Kebbi a fannin kafafen yada labarai Yahaya Sarki, ya fitar, a yau Lahadi, inda yace wannan shine karo na biyu da za’a yi auren da gwmanati ke daukar nauyi a Kebbi.

An sanya ranar 27/02/2025 a matsayin lokacin gudanar da bikin wanda za’a yi a fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu a birnin Kebbi.

Angwaye da amaren zasu samu wannan nasara inda gwamnatin zata dauki nauyin komai na bikin su,.

Kowane ango da amarya zasu samu naira dubu 180,000 a matsayin sadaki da kayan daki da suka hada da gado da katifa da kuma kayan kitchen baki daya.

Tuni an fara tantance Amare da Angwaye a duk fadin kananan hukumomin jihar 21 domin a tabbatar ba’a samu wadanda basu cancanci auren ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here