Manoma da yan kasuwa sun yi kukan karyewar farashin kayan abinci a jihar Niger 

0
119

Shigo da kayan abinci daga kasashen Chadi, Ghana, Jamhuriyar Benin da Burkina Faso, ya rugurguza farashin hatsi a kasuwannin abinci na jihar Niger.

Yan kasuwar sun bayyana cewa sakamakon haka yanzu basa samun ciniki da riba kamar yadda suka yi tsammanin samu. Manoman jihar since sun tara hatsi don cin riba mai yawa sai dai sun shiga damuwa saboda shaguna da kasuwanni sun cika da buhunhunan kayan abinci, amma babu masu siya.

Sun ce farashin buhun da ake siyarwa akan Naira 105,000, a baya yanzu ya koma Naira 80,000.

Yan kasuwa sun ce farashin wake da waken soya da dawa da masara da gero na ci gaba da yin kasa babu kakkautawa, inda suka ce hakan ya samo asali daga yadda wasu kamfanonin sarrafa abinci a kasar nan ke siyan hatsi daga kasashe makwabta saboda suna samun farashi mai rahusa akan yadda ake siyarwa a Nigeria.

Manoma da yan kasuwar sunce abinda yasa ake samun saukin kayan abinci daga wasu kasashen shine amfanin gona ya yi kyau a wadannan kasashe, manoman su suna da damar siyar da hatsin da suka noma a farashin da ya fi araha.

Daya daga cikin manoman Minna yace sun tara hatsi da yawa saboda sun yi zaton farashi zai yi sama don su siyar da abincin da tsada, amma sun ga abun da suke zato ya canja.

Yace dole in zasu siyar da kayan abincin da suka tara a yanzu sai sunyi asara saboda karyewar farashin.

Shugaban Kungiyar Manoma da Masu Samar da Hatsi ta kasa, reshen Karamar Hukumar Shiroro, Hassan Ango Abdullahi, ya tabbatar da hakan a yayin wata tattaunawar da yayi da manema labarai a kasuwar hatsi ta Gwada.

Ya ce, kamfanoni sun fi son siyan hatsi daga Chadi da Ghana da sauran kasashen waje saboda farashin su yana da sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here