Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da Fim din Zarmalulu

0
71

Hukumar tace fina-finai ta Jahar Kano ta dakatar da fim din Zarmalulu tare da gayyatar dukkannin wanda suka fito a cikinsa domin jin dalilin da yasa aka shirya shi.

Daukar matakin ya biyo bayan zargin da aka yiwa mashirya shirin na yin amfani da Kalmar badala a matsayin suna.

Bayanin hakan ya fito cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai, na hukumar tace fina-finai da dab’i ta Jahar Kano Abdullahi Sulaiman, ya fitar.

Sanarwar tace biyo bayan korafin da hukumar ta karba daga wasu mutane akan fim din wanda Shugaban hukumar Abba El-mustapha, ya bayyana damuwarsa tare da dakatar da film din da kuma gayyatar dukkannin wadanda suka fito a shirin domin jin dalilin yin amfani da ita wannan kalma.

Film din “Zarmalulu” ana zargin sa da rashin ma’ana tare da kama da wani suna na badala, a saboda da haka hukumar ta dakatar da shi tare da kira ga dukkannin wanda suka fito a cikinsa dasu bayyana a gaban kwamitin data kafa wanda kin yin hakan ka iya jawo musu fushin hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here