Kawo yanzu dai rundunar yan sandan jihar Anambra, ta kama wani matashi dan kimanin shekara 37 mai suna Kosisochukwu Okafor, akan zargin kisan dan uwansa mai suna Emmanuel Okafor, bayan sun samu rashin fuskanta akan abinci.
Lamarin ya faru a kauyen Adegbe, dake karamar hukumar Njikoka, a Jihar Anambra, ranar Juma’a. Shaidun gani da ido sun ce rashin fahimtar da yan uwan suka samu akan kayan abinci ne dalilin samun rikicin da yakai ga yin kisan.
Karami daga cikin masu fadan shine yayi amfani da wata sanda inda ya dokawa yayan sa a kirji wanda hakan ya sanya shi faduwa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar sa bayan duba lafiyarsa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda reshen Abagana, tare da ‘yan banga na yankin, sun cafke wanda ake zargin da misalin karfe 7 na daren juma’a.