Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola, da jam’iyyar APC ta dakatar kwanakin baya.
Kwankwaso, ya ziyarci Aregbesola, a gidan sa dake jihar Lagos.
Ziyarar tasa tazo a daidai lokacin da sabon shugabancin jam’iyyar NNPP ya sanar da korar Kwankwaso.