Jam’iyyar NNPP ta kori Kwankwaso, Buba Galadima da yan kwankwasiyya

0
203

Jam’iyyar NNPP a matakin kasa ta kori Kwankwaso, Buba Galadima da yan kwankwasiyya.

Jam’iyyar ta kuma sanar da korar daukacin magoya bayan kwankwasiyya.

NNPP ta dauki wannan mataki bayan gudanar da taron ta na kasa daya gudana a Jihar Lagos ranar 4 ga Fabrairu.

Bayan haka an tabbatar da Dr. Agbo Major, a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, tare da bayyana kafa kwamitin gudanar da ayyukan NNPP na kasa.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar NNPP ta kasa da ke Abuja a ranar Asabar, Dakta Major ya jaddada aniyar jam’iyyar ga hukuncin da babbar kotun jihar Abia ta yanke a ranar 1 ga Nuwamba, 2024, wadda ta amince da kwamitin amintattu na jam’iyyar (BOT), karkashin jagorancin Dokta Boniface Okechukwu Aniebonam, har zuwa lokacin da za a warware duk wata rigima ta cikin gida.

Shugaban jam’iyyar ya kuma zargi tsohon gwamnan na jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da magoya bayan kwankwasiyya da yada karya a cikin jam’iyyar da kuma yunkurin kawo mata hargitsi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here