Rundunar yan sandan Nigeria ta kori jami’an ta 3, masu yin garkuwa da mutane

0
37

Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Abia ta sanar da sallamar wasu jami’an ta 3, daga aiki saboda zargin su da aikata laifukan da suka ci karo da ka’idar aiki.

Rundunar ta sanar da daukar wannan mataki ta bakin kakakin ta Maureen Chinaka, cikin wata sanarwa data fitar a Juma’a data gabata.

Sanarwar tace kwamishinan ‘yan sandan jihar Danladi Isa, ne ya bayar da umarnin korar ‘yan sandan saboda wancan zargi.

Yan sandan da aka kora sun hadar da Jonas Nnamdi, James Daniel, da Ifeanyi Emeka..

Chinaka, ta kara da cewa an kori yan sandan ne sakamakon aikata mummunan laifin rashawa da hada baki da wasu don yin garkuwa da mutane, wanda hakan babban laifi ne a tsarin dokokin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here