Yan sanda sun kama manajan bankin daya sace Naira miliyan 650 daga asusun mutane 35

0
30

Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani manajan banki mai suna Adeniyi Talabi, akan zargin sace Naira miliyan 650 daga asusun bankin mutanen dake hulda da su.

Rahotanni sun nuna cewa an sace waÉ—ancan makudan kudade daga asusun masu ajiya da yawan su yakai mutum 35.

Wata Majiya tace a yanzu an dakatar da Adeniyi, tare da wadanda ya hada kai dasu wajen sace kudaden, sannan za’a gurfanar da su a gaban kotu bayan gama bincike don yi musu hukuncin daya dace.

Wannan cigaba yazo bayan da aka samu makamancin labarin hakan, na aikewa da wani Manajan banki a jihar Anambra mai suna Nwachukwu Placidus, zuwa gidan yari, inda zai shafe shekaru 121, a bursin saboda yin wadaka da Naira miliyan 112, na masu ajiya a bankin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here