Fitacciyar yar Gwagwarmaya kuma mai fafutukar samar da jagoranci nagari a Najeriya, Hajiya Naja’atu Muhammad ta zargi wasu magoya bayan mai bawa shugaban Kasa shawara a fannin tsaro Nuhu Ribadu, da yunkurin yi mata barazana.
Daily News 24, ta rawaito cewa Hajiya Naja’atu Muhammad, ta sanar da hakan cikin wani faifan bidiyon data fitar kuma aka yada shi a kafafen sada zumunta.
Tace ta samu kiran waya, daga wasu mutanen da tace mabiyan Ribadu, ne har suna yi mata barazana in har bata janye kalaman da tayi ba, na cewa Nuhu Ribadu, ya taba bayyana shugaban Nigeria Bola Tinubu, a matsayin dan cin hanci da rashawa ba.
Tace babu gudu babu ja da baya, akan kalaman ta saboda gaskiya ta fada, inda tace ta rasa hakurin da zata bayar da kuma wanda za’a bawa hakurin, bisa cewa shi Ribadu ko ya manta da kalaman daya bayyana a kan Tinubu, a baya ne ?