Tinubu ya bawa yar Ganduje mukamin Darakta a hukumar cigaban arewa maso yamma

0
89

Shugaban Kasa Tinubu, ya zabi Asiya Ganduje, yar gidan shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, matsayin darakta daga cikin daraktocin sabuwar hukumar cigaban Arewa maso yamma.

An samu tabbacin nadin cikin wata wasikar da ta samu sanya hannun kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, da mataimakan shugaban majalisar dattawa Barau I Jibril.

Tinubu, ya zabi Asiya Ganduje, a matsayin darakta a fannin cigaban yankunan da al’umma ke rayuwa da kuma karkara. Sai kuma dan gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Aliyu Wamakko, da aka bawa mukamin Darakta a fannin bincike da kididdiga, da Kuma sashin kula da bayanai a hukumar.

Sauran wadanda aka bawa mukaman sun hadar da Khalil Bako, a matsayin shugaban sashin mulki da gudanarwa, sai Mustapha Ahmad Ibrahim, da zai kula da sashin kare lafiyar muhalli, sai Sanusi Bala Turaki, shugaban sashin kudi, yayin da Muhammad Kabir Sani, zai rike sashin shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here