Gwamnan Kano ya dauki nauyin kula da wadanda aka jikkata a Rimin Zakara, tare da umarnin dakatar da rusau a garin

0
27
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da cewa gwamnatin sa zata dauki nauyin kula da lafiyar mutanen da aka jikkata yayin gudanar da rusau a garin Rimin Zakara, dake karamar hukumar Ungogo.

Gwamnan ya sanar da hakan a yau Alhamis, lokacin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar yankin iftila’in daya faru da yan uwan su na rushe gidaje fiye da 50, sai kashe fararen hula da kuma jikkata wasu.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwmanan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Garin Rimin Zakara, dai ya fuskanci tashin hankali a tsakar daren ranar Lahadi, wanda mahukunta suka yi rusau, da hakan ya haifar da rikici tsakanin al’umma da jami’an tsaro.

A yayin jajen gwamna Abba, ya nemi jami’ar Bayero, data dakatar da duk wani shirin rushe garin Rimin Zakara, sakamakon cewa itace ta mallaki wurin da ake wannan takaddamar akai.

Sannan ya nemi jami’an tsaro su dena yin amfani da harsashi mai kisa, ga fararen hula yana mai cewa hakan ba abun amincewa bane.

Gwamna Abba, yace zai gina babban Masallacin juma’a sadakatul jariya, ga mutane 3, da suka rasu a lokacin rikicin rusau din.

Bayan haka yayi alkawarin samar da titi mai kyau a gari, da kuma ruwan sha, sai wutar lantarki, da kuma gina asibitin kula da lafiya a matakin farko.

Wakilin al’ummar Rimin Zakara, Baba Habu Mikail, ya yabawa gwamnan bisa yadda ya nuna damuwar sa ga abin daya faru da yayan garin, inda yace ba zasu manta da karancin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ba.

A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Ungogo, Tijjani Aminu, shima ya yabawa gwamna Abba Kabir, akan yadda yayi gaggawar kulawa da al’ummar da wannan abu ya afku akan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here