Majalisar wakilai ta nemi a kirkiro sabbin jihohi 31 a Nigeria

0
69

Kwamitin majalisar wakilai mai bibiyar kundin tsarin mulkin kasa da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999, ya gabatar da bukatar samar da sabbin jihohi 31, a Nigeria.

Kwamitin ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Alhamis, wanda in haka ta tabbata Nigeria zata kasance mai jihohi 67.

:::Rashin lantarki ya tsananta a Kaduna sakamakon yajin aikin ma’aikatan (KAEDCO)

Bukatar hakan na cikin wata wasikar da aka karanto a zauren majalisar, yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu, ya jagoranta, sakamakon cewa kakakin majalisar Tajuddeen Abbas, baya nan.

Kwamitin wanda Benjamin Kalu, ke jagoranta, yace za’a kirkiro sabbin jihohi 6 a arewa ta tsakiya, sai 4, arewa maso gabas, 5 a arewa maso yamma, sai 5 a kudu maso gabas, 4, a kudu maso kudu da kuma 7 a kudu maso yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here